Rundunar ƴan sanda a jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar jami’inta da ke jagorantar ofishinsu na Wasagu.

Lamarin ya faru a safiyar jiya Laraba a Ɗanmarke da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum a jihar


Sanarwar da yan sanda su ka fitar a yau Alhamis, ya ce jami’an soja a Operation Hadarin Daji ne su ka harbe baturen yan sandan mai suna SP Liman.
An harbe dan sandan a kai a shingen binciken sojin bayan kin gabatar da kansa.
Jagoran sojin a shingen binciken mai suna Hassan ne ya harbe dan sandan.
Jami’an ƴan sanda a Zamfara sun bukaci a gudanar da bincike tare da tabbatar da cewar an hukunta wanda ya aikata hakan.
Sannan sun bukaci shugabannin tsaron da su tabbata an dauki mataki a kai.
Sanarwar ta ce wajibi ne jami’an soji d ƴan sanda a samu fahimtar juna domin samar da tsaro da zaman lafiya.