Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya NEMA ta ce mutane 179 ne su ka mutu a jihohi 15 sakamakon ambaliyar ruwa sama a bana.

Hukumar ta kuma ce ambaliyar ta haifar da rasa matsugunan mutane 208,655 a jihohi 22 a Najeriya.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau, ta ce akwai kadada 107,652 da ruwan ya lalata.

Sannan ruwan ya rushe gidaje 80,049.

Sai dai hukumar ta ce lamarin ya fi ƙamari a jihohin Arewa ne sakamakon kogin Neja da Benue.
Wasu daga jihohin da lamarin ya shafa akwai Kano, Kaduna, Jigawa, Neja, Taraba, Gombe Yobe, Katsina, Nassarawa Bayelsa, Borno, Benue, Ekiti, Akwa Ibom, Ebonyi, Kogi, Oyo, Kebbi, Legas, Kwara, Taraba, Adamawa, Ondo, Sokoto, Bauchi da birnin tarayya Abuja.