Rundunar sojin Najeriya ta nemi haɗin kan hukumomin ƙasar Nijar don yaƙi da ta’addanci a ƙasar.

Babban hafsan tsaron Najeriya Janar Chiristopher Musa ne ya mika rokon yayin ziyarar da ya kai ƙasar jiya Laraba.


Y ce haɗa jai tsakanin ƙasashen biyu zai taimaka wajen yaƙi da ta’addanci da su ka addabi ƙasashen.
Sannan ƙasashen biyu sun amince da yin aiki tare don karfafa dangantaka da magance matsalar tsaro da ke gabansu.
Duk da cewar an samu takun saka tsakanin ƙasashen biyu bayan juyin mulki da aka yi a Nijar, sai dai yanzu kasashen biyu sun amince da ci gaba da aiki tare musamman a bangaren tsaro.
Janar Chiristopher Musa ya ce an ɗauki lokaci ba a tattauna irin wannan ba, a don haka su ka ki ziyarar domin ganin n ci gaba da tattaunawa don magance matsalar tsaron da ke gabansu.