Nigerian soldiers march during 58th anniversary celebrations of Nigerian independence, in Abuja, Nigeria, Monday, Oct. 1, 2018. (AP Photo/Olamikan Gbemiga)

Helkwatar tsaro a Najeriya ta ce ta samu nasarar hallaka ƴan ta’adda 1,166 tare da kubutar da mutane 721 a watan Agusta.

 

Daraktan yaɗa labarai n helkwatar Edward Buba ne ya bayyana haka wanda ya ce daga cikin waɗanda jami’an su ka kashe har da manyan yan bindiga a arewa maso gabashin da arewa maso yammacin Najeriya.

 

Jami’an sun samu nasarar kwato makamai 391, da harsashin bindiga 15,234 da wasu kayayyaki da kuɗinsu ya kai sama da naira biliyan biyar.

 

Sannan cikin watan na Agusta an kwato danyen mai da aka sata mai yawa.

 

A cewarsa, sun ci ƙarfin ƴan ta’adda sosai musamman a yankin arewacin Najeriya.

 

Daraktan ya ce a shirye su ke domin ci gaba da aikin tabbatar da tsaro a ƙasar.

 

Sannan sun buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri domin yaƙi da ƴan bindiga ba abu ne mai sauki da za a magance shi cikin kankanin lokaci ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: