Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai tafi kasar China don ziyarar aiki.

Hakan na kunshe a wata sanarwar da mai bashi shawara kan yaɗa labarai Ajuri Ngelale ya fitar yau.


Sanarwa ta ce shugaba Tinubu zai gana da shugaban ƙasar China Xi Jinping kuma zai tattauna da manyan ƴan kasuwar kasar China.
Tinubu zai samu rakiyar manyan jami’an gwamnati.
Ana sa ran tafiyar za ta taimaka tare da kawo ci gaba musamman ga bangaren tattalin arziƙi a Najeriya.
Tinubu zai ɗan tsahirta a ƙasar Dubai a yayin tafiyar.