Gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahya ya bukaci da kungiyar malaman jami’o’i ta Kasa ASUU da ta janye kudurinta na shiga yajin aiki a Jihar.

Gwamnan ya bukaci kungiyar ne a jiya Alhamis a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar ta ASUU ta jami’ar jihar a gidan gwammati.

Sakataren gwamnatin jihar Farfesa Ibrahim Njodi ne ya wakilci gwamnan a yayin ziyarar kungiyar ta ASUU.

A yayin ziyarar gwamnan ya yi alkawarin biyan alawus-alawus din malaman jami’ar daga ranar Litinin 2 ga watan Satumba, domin janye aniyarsu ta shig yajin aiki da suke shirin yi.

Gwamnan ya bayyana cewa bayan kammala taro majalisar zartaswar Jiyar a ranar Litinin mai zuwa, ana sanya ran kungiyar ta ASUU za ta yanje daga shiga yajin aiki a jihar.

Gwamna Yahya ya shaidawa kungiyar cewa matukar gwamnatinsa ba ta biya kudin alawus-alawus din ba, daga ranar Litinin din, ya yarje da malaman jami’ar da su dauki matakin tafiya yajin aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: