Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta rike albashin likitocin da suka tsunduma yajin aiki a cikin makon nan.

Mai magana da yawun ma’aikatar lafiya ta Kasa Ado Bako ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya fitar.
Bako ya bayyana cewa gwamnatin za ta yi hakan ne, domin tabbatar da dokarta ba aiki, babu albashi, na harna tsawon kwanakin da likitocin suka dauka suna yajin aikin.

Acewar Ado daukar matakin da gwamnatin ta yi ba ya na nufin ta yi watsi ba ne da bukatun kungiyar likitocin, sai dan tabbatar da muhimmancin aikin kiwon lafiya ya ci gaba da dorewa ba tare da samun wani nakasu ga amfanin da al’umma suke da bangaren.

Gwamnatin ta dauki matakin ne a lokacin da take nuna damuwarta, kan matakin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Kasa NARD ta dauka na tsunduma yajin aikin jankunne ga harna tsawon mako daya a ranar Litinin din da ta gabata.
Kungiyar Likitocin ta tsunduma yajin aikin ne domin nunawa gwamnatin bacin ransu kan gaza ceto abokiyar aikinsu, mai suna Dr Ganiyat Popoola da aka yi garkuwa da ita tun a watan Disambar shekarar 2023 da ta gabata.
Sai dai a sanarwar ta Bako ya bayyana cewa a halin yanzu ma’aikatar Lafiya ta Kasa hadin gwiwa da jami’an tsaro na kokarin ganin sun kubtar da jami’ar lafiyar.
Sanarwar ta kuma bukaci da kungiyar ta Likitocin da su koma kan teburin tattauwa domin samar da mafitar da ta dace akan lamarin.