Hedkwatar tsaro ta Kasa ta bayyana cewa jami’anta sun hallaka ‘yan ta’adda 1,166, ya yin da suka kama 1,069 a gurare daban-daban na fadin Kasar.

Mai magana da yawun rundunar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan, a ya yin taron manema labarai a Abuja, kan bayyana irin nasarorin da jami’an suka samu.
Buba ya ce nasarar ta samu ne tun daga farkon watanan na Augusta zuwa yanzu.

Kakakin ya bayyana cewa jami’an sun kuma ceto mutane 721 da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su.

Janar Buba ya kara da cewa daga cikin karin nasarorin da jami’annasu suka samu ciki harda hallaka kwamandojin ‘yan ta’addan da dama.
Ya ce daga cikin ‘yan ta’addan Boko-haram da aka hallaka sun hada da Munir Arika, Sani Dilla (Dan Hausawan Jibilarram), Ameer Modu, Dan Fulani Fari Fari, Bakoura Araina Chikin, Dungusu, Abu Darda da Abu Rijab.
Edward Buba ya bayyana cewa jami’an sun kuma hallaka manyan ‘yan bindiga a yankunan Arewa maso Yamma.
Acewarsa daga cikin wadanda aka hallaka sun hada da Kachalla Dan Ali Garin Fadama, da Kachalla Dan Mani Na Inna, Kachalla Basiru Zakariyya, Sani Bakatsine, Inusa Zangon Kuzi, Ibrahim, Tukur da kuma Kamilu Buzaru.
Sannan Buba ya ce jami’an sun kuma kwato makamai 391, harsasai 15,234, sannan kuma sun dakile haramta satar man fetur na fiye da Naira biliyan 5.