Babbar kotun Jihar Imo ta haramtawa gwamnan Jihar Hope Uzodinma rushe shagunan babbar kasuwar Owerri da yake shirin yi aJihar.

Alkalin kotun mai shari’a I.C Ibeawuchi ne ya yanke hukuncin ne a ranar Alhamis.
I.C ya kuma umarci gwamna Uzodinma tare da wasu mutane biyar, da su dakatar da shirin na rushe shagunan.

Sannan kotun ta kuma dakatar da ci gaba da gina katangar kasuwar, har zuwa lokacin da kotun za ta kammala shari’ar.

Lauyan masu shigar da kara Christian Nwadigo ya bayyana cewa masu shigar da karar sun hada da Incorporated Board of Trustees of Rhema Life, da Ministry International da Sunway Global Properties Limited da dai sauransu.
Lauyan ya ce masu korafi suna bukatar kotun ta dawo musu da kadarorinsu da aka kwace tare kuma da biyansu diyya.