Gwamnan Jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf ya kaddaar da kammala aikin titin Karamar hukumar Ghari da ke Jihar.

Mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar Dawakin Tofa ta bayyana cewa titin mai tsawon kilo mita Biyar, an fara shine tun a zamanin tsohuwar gwamnan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso hawan ta na Biyu, inda kuma bayan hawan gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta yi watsi da aikin.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan zai kammala aikin titin ne domin inganta rayuwar mazauna aikin.

Sanarwar ta kuma ce gwamna Abba ya gargadi dan kwangilar da tsohuwar gwamnatin Kwankwaso ta bai’wa aikin titin gari da ya yi gaggawar dawo da aikin.

Sanarwar ta ambato cewa gwamnan Abba ya ce gwamnatinsa za ta kwace kwangilar daga hannun kamfanin matukar bai ci gaba da gudannar da aikin da aka yarje zai yi ba.

Sanan gwamnan ya bai’wa kamfanin wa’adin mako daya da ya yi gaggawar, kawo kayan aikinsa gurin domin ci gaba da aikin hanyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: