Gwamnatin Jihar Taraba ta bayyana cewa ya zuwa yanzu shirye-shiryen ta sun yi nisa na fara biyan ma’aikatan Jihar Naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi a Jihar.

Gwamnan Jihar Agbu Kefas ya bayyana cewa tuni ya damka ragamar lamarin ga ofishin shugaban ma’aikatan Jihar, kuma a halin yanzu shirin ya fara nisa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da manema labarai bayan sanya hannu da ya yi akan kudirin karin kasafin kudin Jihar.

Gwamnan ya ce bayan shugaban ma’aikatan Jihar da kwamitinsa su sun kammala ayyukansu, bayan sun kawo masa rahoto akan lamarin zai sanya hannu akansa.

Gwamna Kefas ya kuma jinjinawa ‘yan majalisar dokokin Jihar bisa yadda suka amince masa da karin kasafin kudin da ya aike musu ba tare da bata lokaci ba.

Sanna gwamna ya ce gwamnatinsa za ta duk yin komai a bude, tare da tunkari dukkan wasu matsaloli na kudi da suka taso domin cika dukkan alkawurran da ta dauka kafin a zaben gwamnatinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: