Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta bayyana cea wani gini mai hawa daya raftawa wata mata mai shekaru 35 mai suna Balaraba Tijjani da ‘ya’yanta Biyu a unguwar Makwarari da ke Jihar.

Jami’in hulda da jama’a na Rundunar Saminu Yusuf Abdullahi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Kakakin ya ce ginin ya fadowa matar da ‘ya’yan ne sakamakon ruwan saman da aka tafka a Jihar, tun a daren ranar Alhamis har zuwa wayewar garin jiya Juma’a.

Saminu ya bayyana cewa bayan zuwan jami’ansu gurin sun yi nasarar fitowa da matar, da ‘ya’yan nata daga cikin ginin da ya danne su a raye, inda suka kai su Asibitin Murtala Muhammad da ke Jihar.

Jami’in ya ce bayan kuma an kai matar asibitin sun samu labarin rayuwarta, inda kuma ‘ya’yannata Biyu Abdallah mai shekaru 13, da Abdulnasir mai shekaru 11, a halin yanzu su na ci gaba da karbar kulawa a Asibitin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: