Kungiyar agaji ta Duniya International Committee of Red Cross ICRC, ta bayyana cewa mutane 24,000 ne aka tabbata da bacewarsu a Najeriya.

Darektan kungiyar na Afirka Patrick Youssef ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, a yayin bikin ranar tunawa da wadanda suka bace ta duniya, wanda Majalisar dinkin duniya ta sanya ranar 30 ga watan Augusta a matsayin ranar tunawa da mutanen da suka bacewa din.
Kungiyar ta bayyana cewa fiye da rabin mutanen da suka bace yara ne.

ICRC ta ce mafiya yawan mutanen da suka bace matsalar rashin tsaro ne, inda kuma aka kawo mata cigiyar fiye da mutane dubu 10 da su ka bace sakamakon rikice-rikicen mayakan Boko Haram a Jihohin Borno, Yobe, da Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kungiyar ta bayyana cewa a Jihohin da ta ambato masu aikin sa-kai na Kungiyar ta ICRC a Najeriya, sun himmatu wajen sanar da sakonnin kungiyar ga ‘yan uwa da dama da hulda ta yanke tsakaninsu da ‘yan uwansu bisa rikice-rikicen ‘yan ta’adda.
Daraktan ya ce mutanen su na bacewa ne sakamakon garkuwa da su da ake yi, wanda hakan ya ke sanyawa su rasa ‘yan uwansu.