Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta tabbatar da Shehu Dalhatu Tafoki a matsayin zababben dan majalisar wakilai mai wakiltar Kananan hukumomin Faskari, Kankara, da kuma Sabuwa a Jihar Katsina.

Kotun ta bayyana hakan ne a zaman yanke hukuncin da ta yi kan karar da dan takarar jam’iyyar PDP Jamilu Muhammad ya shigar gabanta ya na mai kalubalantar nasarar Dalhatu.
Kotun mai alkalai Uku ta kuma amince da hukuncin da kotun sauraron karrarakin zabe a baya ta Yanke, kan tabbatar da Tafoki a matsayin halastaccen dan majalisar.

Kotun ta bayyana cewa babu kuskure a cikin hukuncin da kotun baya ta yanke akan tabbatar da Tafoki a matsayin dan majalisar ta wakilai.

Yanke hukunci ya kawo karshen ta kaddamar da aka shafe tsawon watanni 27 ana yi akan kujerar kananan hukumomin Jihar ta Katsina.
Shehu Dalhatu ya fara fuskantar matsin lamba ne tun daga zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP, inda abokin takararsa Murtala Isah Kankara ya shigar dashi kara gaban kotu.
Inda a ya yin sauraran kararar kotun ta koli ta tabbatar da Shehu Dalhatu Tafoki a matsayin tabbataccen dan takarar jam’iyyar APC.
Bayan tabbatar dashi a matsayin dan majalisar, Tafoki ya mika godiyarsa ga gwamnan Jihar ta Katsina Malam Umar Dikko Radda bisa goyan bayan da ya bashi.