Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ta bai’wa iyalan baturen ‘yan sandan Jihar mai suna Halliru Liman da wani soji ya hallaka a Jihar Zamfara tallafin naira miliyan daya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Nafi’u Abubakar ya fitar a jiya Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan Jihar ta Kebbi Bello M Sani ne ya mika tallafin ga iyalan jami’in nasu a madadin sauran jami’an rundunar.

Acewar Abubakar an ba su tallafin ne domin a rage musu radadin halin da suke ciki na rashin jami’in, kafin daga bisa a ba su hakkokinsa na aiki.

Kakakin ya ce bayan afkuwar lamarin Kwamishinan ‘yan sandan Jihar tare da wasu daga cikin jami’an rundunar, sun kai ziyarar jaje gidan mamacin da ke cikin Ƙaramar Hukumar Wamakko ta Jihar Sokoto.
Idan baku manta ba dai a ranar Larabar da ta gabata ne wani jami’in tsaron soji, ya harbe jami’in dan sandan a wani shingen binciken ababawan hawa da ke Jihar Zamfara.
Bayan faruwar lamarin, a cikin wata sanarwa da rundunar ’yan sanda ta Jihar ta Zamfara ta fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a garin Danmarke da ke Karamar Hukumar Bukuyum ta Jihar da misalin karfe 10:30 na ranar Laraba.
A lokacin da Baturen ‘yan sandan ke kan hanyarsa ta zuwa wani taro a Jihar.