Al’ummar Najeriya na kokawa bayan da aka wayi gari da ƙarin farashin litar man fetur.

 

Gidajen mai mallakin kamfanin mai na NNPC na siyarda lita guda kan naira 897 zuwa sama.

 

Bayan ƙarin da aka samu a gidan man na NNPC sauran gidajen mai sun ƙara farashin litar zuwa 1200 zuwa sama.

 

Ko da ake zargin gwamnatin tarayya da umartar kamfanin don ƙara farashin litar man, gwamnatin ta musanta.

 

Mutane dai na fargabar ƙaruwar farashin kayayyaki da sufuri sanadin hauhawar farashin litar mai da aka samu daga yau.

 

Wannan na zuwa ne bayan da aka yi zanga-zangar sadar rayuwa da yunwa wanda daga cikin bukatun akwai batun neman rage farashin litar mai tare da mayar da tallafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: