Hukumar kare haƙƙin masu siya da siyarwa a Najeriya ta ce ba ta da shirin daidaita farashin kayayyaki a halin yanzu.

 

Hakan na kunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Ondaje Ijagwu ne ya bayyana haka ba su samu umarnin daidaita farashin kayayyaki a ƙasar ba

 

Wannan na zuwa ne bayan da ƴan kasuwa da masu ruwa da tsaki a bangaren su ka nuna damuwa dangane da zargin hukumar n yuwuwar fitar da daidaitaccen farashin kayayyaki.

 

Sanarwar ta ce fitar da farashi ba haƙƙin hukumar ba ne, aikinsu shi ne tabbatar da gaskiya a cikin kasuwanci.

 

Hukumar ta kuma yi watsi da raderadin da ake yi cewar su na shirin daidaita farashin kayayyaki a Najeriya.

 

Dangane da batun da shugaban kamfanin BUA Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u ya yi kan cewar su na siyar da siminti buhu guda kan naira 3500 amma ana siyar dashi naira 7000 zuwa 8,000, hukumar ta ce ta na yin duk mai yiwuwa don gano inda barakar ta ke.

 

Sannan ta sake jaddada cewar ba su da niyyar shiga hurumin yan kasuwa illa tabbatar da cewar ba a cutar da masu saye ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: