Kungiyar tuntuba ta Arewa Consultative Forum sun ne yankin arewa bai taɓa tsintar kansa a halin da ake ciki ba a yanzu a tarihi.

 

Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar Bashir Muhammad Dalhatu ne ya bayyana haka wanda ya ɗora alhakin ga shuwabannin arewa.

 

A sakamakon haka ne ma ƙungiyar ta bukacesu da su sauya salo don fuskantar kalubalen da arewa da ma Najeriya ke fuskanta.

 

Yace yankin arewa na buƙatar sauye-sauye da za su taimaka wajen fita daga halin da ake ciki.

 

Sannan ya buƙaci a yi sauye-sauye a kundin tsarin mulkin ƙasar domin gaba.

 

Shugaban ya yi wannan jawabi ne a wajen taron da aka yi yau a Kaduna.

 

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci taron akwai tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Tanko Almakura da tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Adamu.

 

Sauran akwai Sanata Kabiru Gaya, Janar Halilu Akilu da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido.

Leave a Reply

%d bloggers like this: