Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun ɗauki alhakin hallaka mutane a jihar Yobe.

A wata wasika da mayaƙan su ka fitar yayin da ake jimamin hallaka mutanen, sun ɗauki alhakin kai harin tare da bayyana dalilinsu.


Wasikar wadda aka tubuta a harshen larabci, su ka ce sun hallaka mutanen ƙauyukan ne saboda bayanai da su ke bai wa jami’an soji tare da hallaka mayaƙan.
A wasikar sun gargaɗi mutanen kan bayanan dasu ke bai wa jami’an tsaro.
Su ka ce babu ruwansuda dukiya ko kai musu hari ko hanasu al’amuran yau da kullum, amma bayanan da su ke baiwa jami’an soji ba zai bari su ci gaba da zama lafiya ba.
Wasikar ta ce wannan hari dasu ka kai gargaɗi ne don kiyayewa a gaba.
Maharan dai sun hallaka mutane da ake kyauta zaton sun kusa 100, yayin da aka sallaci wasu 37 a safiyar yau.
An kai harin ne a yammacin ranar Lahadi.