A cewar kamfanin, a halin yanzu man fetur na nemawa kansa farashi ne a kasuwa.

Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce fetur da kansa ne zai nemawa kansa farashi a kasuwa.

A wata tattaunawa da aka yi da mataimakin shugaban kamfanin na ƙasa Mista Adedapo Segun, ya ce kundin tsarin mulki bai ƙayyade waɗanda za su tsayar da farashin man fetur ba.

A cewarsa, saahe na 205 da ya kafa kamfanin, ya bashi damar sakin fetur don nemawa kansa farashi a kasuwa.

Ya ƙara da cewa dangane da tsadarsa da mutane ke kokawa, batu ne da ya shafi chanjin kuɗaɗe.

Amma ya ce su na ƙoƙarin su da dilallan man na ƙasa don ganin an magance karancinsa.

Kuma ya sake tabbatarwa da ƴan Najeriya cewar, nan da kwana ƙalilan za a kawo ƙarshen matsalar ƙarancin man baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: