Gwamnatin tarayya a Najeriya ta ce mutanen da su ke da lambar zama ɗan ƙasa ta NIN ne kaɗai zasu amfana da shinkafar da za ta siyar naira 40,000 buhu guda

 

Ministan harkokin noma Abubakar Kyari ne ya bayyana haka yayin da yake kaddamar da tsarin wanda aka karyar da farashin don saukakawa yan kasar.

 

Kyari wanda ya wakilci shugaba Bola Tinubu ya ce za a siyarwa da duk magidanci guda buhun shinkafa.

 

Sannan buhu guda mai nauyin kilo 50 za a siyar naira 40,000.

 

Ministan ya ce an fara siyar da shinkafar daga jiya Alhamis kuma waɗanda ke da lambar zama ɗan ƙasa ne kaɗai za su ci gajiyar tsarin.

 

Ministan ya alakanta tsadar kayan abinci da yunwa da ake ciki da annobar korona da kuma yaki tsakanin Rasha da Ukraine.

 

Sai dai wadanda ke aikin gwamnati su ke tsarin biyan albashi za a siyarwa da shinkafar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: