Jami’an tsaron hukumar farin kaya ta DSS ta kama shugaban ƙungiyar ƙwadago a Najeriya NLC Joe Ajaero.

Rahotanni sun nuna cewar an kama shugaban ne yau a filin sauka da tashin jiragen sama na Abuja.


Shugaban NLC na kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Burtaniya don halartar taron taron ƴan kasuwa wanda za a fara a yau.
Sai dai ba a bayyana dalilin kama shugaban ƙungiyar ba.
Idan za a iya tunawa jami’an ƴan sanda a baya sun gayyaci shugaban kan zargin ta’addanci.
Da yake tabbatar da kamawar, mai magaa da yawun hukumar Benson Upah ya ce ba su san inda aka tafi da shugaban nasu ba.
A makon da ya gabata ne dai shugaban ya halarci gayyatar da yan sanda su ka yi masa.
Gwamnatin tarayya ta musanta zargin da ake yi mata na karin kudin haraji a VAT ba.
Ministan kudi Wale Edun ne ya bayyana hakan a safiyar yau Litinin, inda ya ce har yanzu harajin VAT yana nan a kan kashi 7.5% na farahsin kayayyakin da tsarin ya shafa.
Ministan ya bayyana cewa babu kanshin gaskiya a cikin rahotannin da ake yadawa akan karin harajin daga kaso 7.5 zuwa kaso 10.
Wale ya bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa kan karin haraji wajen cinikayyar kayayyaki a Kasar.
Ministan ya kara da cewa koƙarin da gwamnatin Kasar ke yi ne na samarwa da ‘yan Kasar sauƙin ne akwanakin baya ta dakatar da karɓar harajin shigo da wasu kayayyaki daga kasahen ketare.