Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bai wa hukumar bayar da agajin gaggawa umarnin kai agaji a jihar Borno.

Hakan na kunshe a wata sanarwar da mai bashi shawara na musamman kan yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar


Tinubu ya bai’wa hukumar umarnin kai ɗauki kai tsaye ga mutanen da ibtilain ya shafa.
Sannan ya yi umarni da a gaggauta kwashe mutanen daga wuraren da ambaliyar ta shafa.
Tinubu ya sha alwashin tallafawa jihar da dukkanin abinda su ke buƙata.
Ambaliyar dai ta raba dubban mutane da matsugunansu.
Kuma ta fara ne a daren jiya bayan ruwan saa da aka yi kamar da bakin ƙwarya.