Rundunar ƴan sandan Najeriya za ta aike da jami’anta 35,000 jihar Edo domin bayar da tsaro a yayin zaɓen da za a yi a jihar.

Babban sefeton ƴan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ne ya bayyana haka yau ya ce za a yi zaɓen a ranar 21 ga watan Satumba.


Kayode ya ce sauran jami’an tsaron da za su yi aikin sa idon sun kai 80,000.
Sufeton ya ƙara da cewa sauran jami’an tsaro na jihar ba za su bayar da gudunmawar a zaɓen ba.
Shirye-shiryen jami’an na zuwa ne bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce ta shirya tsaf don gudanar da zaɓen
Sufeton ya aike da gargaɗi kan cewar ba za su saurarawa kowanne mutum ko kungiya da su ka yi ƙoƙarin kawo targarda a yayin ko kafin da ma bayan zabe a jihar ba.