Jam’iyyar APC a Jihar Sokoto ta lashe dukkan zaben kananan hukumomi 23 na fadin Jihar wanda aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

Shugaban Hukumar Zaben ta Jihar Aliyu Suleiman ne ya tabbatar da hakan a yau Litinin.

Shugaban hukumar ya ce ’yan takarar jam’iyyar ta APC a kananan hukumomin Jihar, tare da dukkan kansilolin da suka tsaya a jam’iyyar.

A yayin zaben kananan hukumomin jam’iyyu 15 ne suka kara a yayin zaben.

Tuni dai hukumar ta mikawa dukkan zababben shugabannin kananan hukumomin shaidar cin zabe.
Daga bisani kuma a yammacin yau din suka karbi rantsuwar kama aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: