Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bai’wa gwamnatin Jihar Borno tallafin kayan rigakafin cutar Kwalara domin yiwa waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa a garin Maiduguri a Jihar rigakafi.

Jami’in hukumar mai kula da harkokin kiwon lafiya a Jihar ta Borno Dr Walter Kazadi Molumbo ne, ya bayar da kayan tallafin gwamnatin Jihar.
Kayan tallafin Sun kunshi na’urorin gwajin cutar ta kwalara guda biyar, na’urorin SAM guda 14, da kuma sauran kayayyakin jinya domin tallafawa gwamnatin jihar a daukar matakan da take yi na magance afkuwar cutar a Jihar.

Jam’in hukumar ya kuma ce na’urorin tantance cutar za su taimaka matuka wajen yin rigakafin cutar ta kwalara da kuma magance ɓarkewar ta.

Har ila yau ya kara da cewa na’urorin za kuma su taimakawa ma’aikatan kiwon lafiya wajen yaki da matsalar karancin abinci mai gina jiki a tsakanin yara, don samar musu da kyakkyawar rayuwa.
WHO ta ce kowane daya daga kayan gwajin cutar zai iya gwajin mutane 100.
Kazalika ya ce na’urorin SAM kuma guda 14 za su samar da muhimman kayayyakin jinya domin kula da yaran da ke fuskantar matsalar karancin abinci mai gina jiki.
Sannan hukumar ta kuma jajantawa gwamnatin da kuma matanen Jihar bisa ambaliyar ruwan da aka samu a Jihar.