Tsohon shugaban Najeriya Chief Olusegun Obasanjo ya yi gargadi kan cewar matuƙar ba a kawar da matsalar yara da ba sa zuwa makaranta ba matsalar tsaro za ta ci gab da wanzuwa a ƙasar.

Obasanjo ya bayyan haka ne yayin da ya halarci wani taro a Ibadan.
Ya ce muddin ana son samun nasara a kn sha’anin tsaro da ƙasar ke ciki wajibi ne a yi waiwaye kan yara da ba sa zuwa makaranta da kuma rashin aikin yi da talauci.

A cewarsa, sai an yi yaƙi da hakan da gaske kafin cimma gaci.

Obasanjo ya ce a halin yanzu akwai yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.
Ya ce muddin aka ci gaba da tafiya a haka babu wani cigaba da za a samu illa koma baya.
Kuma matsalar ce ta sa aka tsinci kai a halin da ake ciki a yanzu.
Ya ce wajibi ne a yi duba a kai muddin ana son magance garkwa da mutane matsalar tsaro da sauran munanan ayyuka.