Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta tilasta gwamnatin tarayya don bincike a kan zargin da ake yi wa tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma karamain ministan ilimi Bello Matawalle kan zargin alaka da yan ta’adda.

Hakan ya biyo bayan korafin da wani dan kishin kasa Abubakar Dahiru ya shigar a gaban kotun.

Kotun dai ta umarci shugaba Bola Ahmed Tinubu da babban lauyan gwamnatin tarayya da ma’aikatar Shari’a da babban sufeton yan sanda na ƙasa.

Kunshin karar dai ya bukaci kotun ta tilasta shigaban ƙasa baiwa babban sufeton yan sanda umarnin bincike a kan zargin da ake yi wa Matawalle

Haka kuma a korafin aun buƙaci shugaban ƙasa da ya sa a binciki matawalle da ayyukan ta’addancin da ake yi a jihar Zamfara.

Tun tuni dai ake zargin Bello Matawalle da hannu cikin ayyukan hare-haren da ake kai wa a jihar Zamfara.

Ko a makon da mu ke ciki ma sai da gwamnan jihar Dauda Lawal Dare y mika korafin ga mashawarcin shugaban ƙasa kan tsaro Malam Nuhu Ribadu.

Haka kuma gwamnatin ta ce a shirye ta ke don fitar da hujjoji kan zagezargen da ake yi wa Matawalle.

Leave a Reply

%d bloggers like this: