Al’ummar ƙauyen Jika da Kolo da ke ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna sun zargi jami’an sojin saman Najeriya da yi hallaka mutane a masallaci a wani hari da su ka kai ta sama.

Mutanen sun ce sojin sun kai musu hari ne a ranar Juma’a wanda ake zargi mutane 23 sun rasa ransu


Mutanen kauyen sun ce an kaiwa mutanen ne hari su na tsaka da salla a masallaci
Sai dai jami’an sojin saman sun ce babu masallaci a wajen da su ka kai hari.
Wani da ya zanta da jaridar Daily Trust ya ce mutanen da su ka mutu akwai manoma da yara.
Sai dai jami’an sojin saman sun musanta.
Mau magana da yawun jami’an Kabiru Ali harin da su ka kai sun kai ne mabiyar yan bindiga