Rundunar sojin sama a Najeriya ta ce ta fara bincike a kan zargin harin bam da aka jefawa masallata a jihar Kaduna.

Daraktan yaɗa labarai na rundunar Kabiru Ali ne ya shaida haka a wata sanarwar da ya fitar yau Litinin.


Sai dai ya sake musanta zargin wanda ya ce harin da aka kai kan ƴan bindiga ne kuma ba a kai wa masallata ba.
Ana zargin jami’an sojin saman Najeriya da jefa bam kan masallata a ƙauyen Jika da akilo da ke yankin Yadin Kidandan a karamar hukumar Giwa ta jihar.
Kusan mutane 25 ake zargi sun rasa ransu wanda daga ciki akwai yara ƙanana.
A ɓangaren jami’an kuwa sun musanta kai wa masallatan hari yayin da su ke tsaka da salla a ranar Juma’a.