Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu Sanata Ali Ndume ya bukaci shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya yi amfani da sojin haya don murkushe mayaƙan Boko Haram.

Ndume ya ce amfani da sojin hayar zai saukaka hanyar murkushe mayakan cikin sauƙi.
Duk da cewar ya yabawa jami’an soji da ƴan sa kai, amma ya ce ba za su iya gidanar da aikin ba saboda ba su da isassun kayan aikin da ya kamata.

Ndume ya ce idan aka yi amfani da sojin haya cikin kankanin lokaci Boko Haram za ta zama tarihi.

Wannan dai na zuwa ne bayan da mayakan su ka kai wani sabon hari a Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza a jihar.
A yayin harin, mayaƙan sun yi wa wasu manoma shida yankan rago yayin dasu ka yi garkuwa da mutane biyar ciki har da mata.
An kai harin ne yayin da manoma ke tsaka da aikin girbe amfanin gona.