Fitaccen mai garkuwa da mutanen nan Bello Turji ya ce shi ba ya tsoron mutuwa ko a kasheshi.

Turji kuma bukaci a yi sulhu domin samar da zaman lafiya a jihar Zamfara.


Bello Turji na daga cikin ƴan bindiga da helkwatar tsaro ta ayyana nemansu ruwa a jallo.
A faifen bidiyon da Turji ya fitar ya tabbatar da kisan mai gidansa Halilu Sububu, ya ce kisan nasa ba zai sa ya yi shiru ba.
Turji ya ce a shirye yake ya ajiye makamansa muddin gwamnati ta shirya tattaunawa da shi.
A cikin bidiyon Turji na nuna kaduwarsa kan kisan mai gidansa Halilu Sububu.
Ta na mai cewa ba shi kadai aka fara kashewa ba kuma shi ma ba ya tsoron mutuwa.