Wasu da ake kyauta zaton yan bindiga ne sun tarwatsa masu sallar juma’a a jihar Katsina.

Yan bindigan dauke da muggan makamai sun shiga kauyen Dan Ali da ke karamar hukumar Danmusa su ka tarwatsa masallata.

Maharan sun shiga su na harbe-habe lamarin da ya sa masallatan su ka tsere.

Wani mazaunin garin ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce sun fara jin harbe-harben ne lokacin da su ke shiri fara sallar juma’a a yau.

Da jin harbe-harben ne kuma su ka tsere lamarin da ya sa ba a yi sallar juma’ar ba.

Mutumin ya ce jami’an tsaro sun yi kokarin tarwatsa su, sai dai akwai bukatar karin jami’an domin su na cikin fargaba.

A cewarsa an yi garkuwa da da yawa daga cikin manoma a garin a sakamakon haka ne ma su ke tsoron zuwa gonakinsu.

Zuwa yanzu dai ba a samu ji daga jami’an yan sanda ajihar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: