Aƙalla kujeru 22 jam’iyyar Action Peoples Party APP ta lashe daga cikin kujeru 23 na ƙananan hukumomin jihar Rivers.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Jusctice Adolphus Enebeli ne ya sanar da sakamakon zaben a yammacin yau a Fatalkwal babban birnin jihar

Ya ce zai sanar da sakamakon zaben karamar hukumar Etche a nan gaba domin har yanzu ana ci gaba da irga kuri’a.

Haka zalika zuwa nan gab za a sanar da sakamakon zaben kujerun kasilolin bayan an kammala irgawa.

An dai gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi an jihar Rivers ne yau duk da cewar jami’an ƴan sanda sun jnye jikinsu daga zaben.

Jami’an sun ce sun janye daga zaben ne don biyayya ga umarnin kotu da ta yanke hukunci a ranar 30 ga watan Satumba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: