Rundunar ƴan sandan jihar Nassarawa ta kama wasu yan fashi fa makami tare da kwato karyaki har da makamai.

 

Mai magana da yawun rundunar Ramhan Nansel ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi.

 

Jami’an sun kama wani Salim Hussaini mai shekaru 22 da Abdulkadir Musa da wani Dimas Danja.

 

Sannan an samesu da wasu makamai.

 

Sanarwar ta ce wadada aka kama yara ne ga wani tawagar yan fashi da ka addabi yankunan Mararraba.

 

Tuni aka fara gudanar da bincike a kansu.

 

Rundunar ta kuma kama wasu mutane da wata motar sata kuma yanzu ake binciken wanda ya siyar musu.

 

Jami’an sun bukaci mai motar da y je don gabatar da hujjojinsa tare da karbar motarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: