Hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima NYSC ta ce a halin yanzu abu shirin fara biyan naira 77,000 a matsayin alawus ga masu yi wa kasa hidima.

Babban darakta a hukumar Birgediya Janar Yushau Ahmed ne ya bayyan haka ya ce har yanzu naira 33,000 za a dinga biya.


A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce har yanzu ba a fitar da jadawalin biyan karin da aka yi ba.
A don aka za a ci gaba da biyan naira 33,000 ba naira 77,000.
A cewar daraktan, duk da cewar gwamnati ta amince da ƙarin, amma ba a fitar da kudaden da za a biya ba.
Ya ce ba ma iya mambobin da ke yi wa kasa hidima ba, hatta maaikatansu an yi musu karin albashi tun watanni hudu zuwa biyar, amma ba a fara biya ba.
Ya ce babu lokacin da za a fara biyan karin da aka yi domin ba a fitar a hukumance ba.