Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya Malam Ahmad Gumi ya ce ya na samun ƴan rakiya daga bangaren gwamnatin a duk lokacin da a je yin sulhu da yan bindiga.

 

Gumi y sake jaddada buƙatar samar da zaman lafiya da yin sulhu da yan bindiga.

 

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar The Punch, Gumi ya ce a kowanne lokaci idan zai shiga tsakanin ƴan bindiga da gwamnati, ya na samun Yan rakiya daga bangaren gwamnati da shugabannin gargajiya.

 

A cewarsa, bai taba yin wani abu kansa tsaye ba tare da mukarraban gwamnati ba.

 

Daga cikin waɗanda su ke zuwa tare har da yan sanda.

 

Dangane da zargin da ake yi cewar yan siyasa ne ke daukar nauyin yan bindiga, Gumi ya musanta tare da cewar babu wani dan siyasa da yake daukar nauyin yan bindiga.

 

Ya ce bukatun da su ke so yan bindiga sun fada har a kafofin yanar gizo wanda kowa ya gani.

 

Ya ce har yanzu ya na goyon bayan zama da su a yi sulhu da su domin samar da zaman lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: