Kungiyar Ma’aikatan manyan kamfanoni da hukumomin gwamnati da ke karkashin kungiyar TUC, sun tsunduma yajin aiki a hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Kasa NAFDAC da ke birnin tarayya Abuja.

Kungiyar ta tsunduna yajin aikin ne sakammakon gazawar hukumar ta NAFDAC wajen kawo karshen matsalolin da suka shafi jindadin ma’aikata da kuma kara musu girma.


A wata sanarwa da kungiyar ta fitar tun a ranar 4 ga watan Oktoba nan, ƙungiyar ta ce ta fara yajin aikin ne biyo bayan tattaunawa da shugabancin hukumar ta NAFDAC.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, kungiyar na nema ƙarin girma, albashi, da kuma jindadin ma’aikata, amma hakan ya gaza samuwa tun bayan shigar da bukatunsu.
Sanarwar wadda Sakataren kungiya TUC na Kasa Kwamared Ejor Michael ya sanya wa hannu ya umarci dukkan ma’aikatan da su tsuduma yajin aikin daga yau Litinin.
Ƙungiyar ta kara da cewa kafin shigar ta yajin aikin sai da ta sanar da shugabancin hukumar ta NAFDAC aniyarta tun a ranar 20 ga watan Satumba a wasu taruka da suka gudanar, tare da ba su wa’adin kwanaki 14 da su yi gaggawar magance matsalolin kungiyar amma hakan ya gagara.
Sakataren ya kara da cewa baya ga gaza yin komai akan lamarin kungiyar ta sake gudanar da taro a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ta cimma matsayar tafiya yajin aikin a yau a fadin Kasar.
Ƙungiyar ta kuma bukaci daukacin ma’aikatan da su dakatar da dukkan ayyukansu, tare da kwashe kayyakinsu sakamakon cewa ba za a sake bari kowa ya shiga ofisoshin hukumar ta NAFDAC ba a lokacin da ake yajin aikin.
Uwar kungiyar ta umarci dukkan shugabannin kungiyar na Jihohi da yankuna da su tabbatar da ganin ma’aikatan sun bi umarnin shiga yajin aikin.