Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta tallafa wa alhazan shekarar 2025 mai zuwa ba.

Hukumar ta bayyana cewa mafi akasarin tallafin da gwamnati ke bayarwa na zuwa a matsayin rangwame ga maniyyata wajen samun dala a farashi mai sauki daga bankin Kasa na CBN.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar.

Sanarwar ta ce gwamnatin ta tarayya ba za ta iya ci gaba da bayar da rangwame na kudin aikin Hajji ba ga maniyyata ba, ko da a karkashin ma’aikatan zuwa Hajji na masu zaman kansu ko kuma na gwamnati.

A sanarwar hukumar ba ta kayyade iyakacin kudin da maniyyatan za su biya ba na shekarar 2025, amma hukumomin jin dadin alhazai na Jihohi sun bukaci maniyyatan da su fara ajiye Naira miliyan 8.5.

Leave a Reply

%d bloggers like this: