Gwamnatin tarayya ta bayyana bude shafi da matasan kasar za su iya samu Keke Napep wato adaidaita Sahu mai amfani da iskar gas ta CNG wanda za ta bayar nan bada jimawa ba.

Ma’aikatar ci gaban matasa ta Kasa ce ta tabbatar da aniyyar gwamnatin akan matasan, inda za su ciki fom ta shafinta na intanet domin samun tallafin.

Karamin ministan bunkasa matasa Kwamred Ayodele Olawonde ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na X a jiya Litinin, bayan kaddamar da shafin da matasan za su iya mallakar adaidaita Sahun.

Karamin ministan ya ce ta shafin da aka bude ne kadai matasa za su iya haduwa da masu aiki kai tsaye ta shirin P-CNG yayin da suke kokarin mallakar abin hawan.

Karamin Ministan ya kara da cewa an samar da shafin ne domin bai’wa matasan Kasar damar mallakar adaidaita sahun, tare da sauran shirye shiryen da ya shafi ma’aikatar.

Ministan ya ce ga dukkan wanda ke da sha’awar mallakar Adaidaita Sahun za su shiga shafukan Ma’aikatar na intanet kamar haka: www.youthcng.ng.

Ayodele ya ce manufar shirin da gwamnatin shugaban Tinubu ta samar na Renewed Hope shi ne rage yawan matasa marasa ayyukan yi a fadin kasar.

Ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu na da nufin bunkasa matasan kasar ta hanyar ba su horo kan sana’o’i da kuma ba su kayan jari domin dogaro da kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: