Gwamnan Zamfara Dauda Lawal Dare ya bayyana cewa ana ci gaba da samun nasara kan matsalar rashin tsaro a jihar bisa hallaka wasu shugabannin ƴan ta’adda da aka yi a Jihar.

Gwamna ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a wata ganawa da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a fadar shugaban Kasa da ke Abuja.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa na yin iyakar bakin ƙoƙarinta domin magance matsalar rashin tsaron da ta addabi fadin Jihar.

Gwamna Dauda ya ce su na yin iyaka bakin yinsu na tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar,amma makomar mutanen na hannun Allah.

BDauda ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta gajiya ba har sai lokacin da ta kawo karshen ‘yan ta’adda a Jihar.
Gwamnan ya ce sun mika dukkan lamarinsu ga Allah akan lamarin Jihar, kuma shi zai yi wa Jihar maganin matsalarta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: