Gwamnatin Jihar Jigawa karkarshin jagorancin Malam Umar Namadi ya musanta amincewa da mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikatan Jihar.

Gwamnatin ta musanta hakan ne ta cikin wani saƙon murya da babban mai bai’wa gwamnan shawara kan harkokin albashi da fansho Ado Kazaure ya fitar, tare da janye kalamansa da kuma musanta amincewar gwamnan kan karin mafi karancin albashin.

Kafin musanta batun tun da fari dai babban mai ba Gwamnan Jihar shawara na musamman kan harkokin albashi da fansho Malam Ado Kazaure, ya sanar da amincewa da mafi ƙarancin albashin.

Daga baya kuma ya sake fitar da wani sakon murya na musanta kalaman da yayi ya fara biyan ma’aikatan mafi karancin albashin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: