Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Umar Damagum ya bayyana cewa ‘yan Kasar da suka sayar da kuri’unsu akan karbar abinda bai taka kara ya karya ba a lokacin zaben shekarar 2023 su ne suka fi shiga kangin wahala a halin yanzu a Kasar.

Damagun ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, bayan kammala wata ganawar sirri da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Abuja.

Mukaddashin shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa ‘yan Kasar da ke goyon bayan gwamnatin Shugaba Tinubu ne ke cikin kangin wahala sakamakon sayar da ‘yancinsu ta hanyar karbar taliya da atamfa da dai sauransu.

Damagun ya kara da cewa jam’iyyar APC ba ta bata yin wani shirin karbar mulki ba a Kasar, don haka kuwa babu wani abu da za a karba daga garesu.

Shugaban ya bayyana cewa ya zama wajibi mu nemo shugabanni masu nagarta waɗanda suka shirya jagorancin Kasar da gaske.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: