Akalla manoma hudu ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu kuma suka jikkata ta cikin wani sabon hari da aka kai wajen hakar ma’adanai a yankin Butura da ke ƙaramar hukumar Bokkos ta Jihar Filato.

Shugaban kungiyar matasan Butura Sabastine Majit ne ya tabbatar da faruwar lamarin a garin Jos babban birnin Jihar a yau Asabar.

Shuganan ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na daren ranar Alhamis.

Shugaban matasan ya bayyana cewa hari ya faru ne kwanaki huɗu bayan kai wani hari kauyen Wumat, inda aka hallaka mutane biyar ‘yan gida ɗaya, ciki kuma har da wata mata mai juna biyu.

 

Acewar Sabastine a cikin wata guda da ya gabata, an hallaka fiye da mutane 20 a yankinsu a wasu hare-haren da daban-daban da a ka kai.

Har ila yau ya ce yankunan Barikin Ladi, Riyom, Bassa, Jos ta Arewa, Jos ta Kudu, Wase da kuma Mangu, yankunan na ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a cikinsu.

Shugaban kungiyar matasan ya ce matukar hukumomin da abin ya shafa ba su ɗauki matakin kawo ƙarshen hare-haren ‘yan ta’addab ba, mutanen yankunan za su dauki makamai domin kare kansu daga hare-haren.

Leave a Reply

%d bloggers like this: