Hukumar gudanarwar babban birnin tarayya Abuja, karkashin ministan birnin Nyesom Wike ta kaddamar da rushe wasu gidaje 50 a birnin.

Daraktan sashin kula da ci gaba birnin Mukhtar Galadima ne ya jagorancin kaddamar da rusau din a jiya Alhamis.
Hukumar ta kadamar da rusau din gidaje 50 din a yankin sabin Lugbe, wadanda aka ginasu ba bisa ka’ida ba.

Hukumar ta ce masu kwacen filaye sun yi gine-gine ba tare da sahalewar hukumomin da abin ya shafa ba.

Muktar Galadima ya bayyana cewa yankin Kudu maso Yamma na Sabon Lugbe ya fada cikin yankin Phase 5 na babban birnin tarayya.
Acewarsa hukumar za ta dakile masu satar filaye, inda kuma ta shawarci masu son saye filayen da su tabbatar da sahihancin kadarori kafin biyan kudin.
Hukumar ta fara rusau din ne da gidaje 10, inda ta kuma bayyana aniyar ci gaba da ragowar.