Ministan tsaro a Najeriya Mohammed Badaru Abubakar ya yabawa jami’an sojin kasar wajen kakkabe ayyukan yan bindia a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Ministan ya jinjinawa jami’an ne yayin da ya ziyarci sarkin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Maigwari ll tare da duba wasu kayan aikin soji ciki har da helkwatar sojin.


Badaru ya ce ana samun nasara a ayyukan da sojin ke yi.
A cewarsa, watanni shida kenan ba a samu rahoton ta’addanci a yankin ba.
Badaru ya yabawa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu sannan ya bukaci jami’an sojin da su ci gaba da dagewa don ganin an kakkabe bata garin.
Ya ce ko da ziyarar da ya kai musu ya yi ne don karfafa musu gwiwa a kn ayyukan da su ke yi.