Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da aikin hanyar karamar hukumar Tofa da ke Jihar.

Gwamna ya bayyana hakan ne ta cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook a yau Laraba, ya ce ya kaddamar da aikin ne a daren jiya Talata.

Gwamnan ya ce hanyar mai nisan kilo mita biyar, an kuma sanya mata wutar lantarki mai amfani da hasken rana, wanda hakan zai taimaka wajen bunkasar harkokin Kasuwanci a Karamar hukumar.

Gwamna Abba ya kara da cewa gudanar da titin na daya daga cikin ayyukan da ya dauko domin raya yankunan karkara.

Acewar Abba aikin zai taimaka wajen rage yawaitar masu shigowa birane daga yankunan karkara.

Gwamnan ya kuma mika godiyarsa ga dukkan mutanen Karamar hukumar ta Tofa bisa karbar da suka yi masa shi da tawagarsa.

Sannan gwamna ya kuma mika godiyar ga Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe wanda shi ne wakilin Karamar hukumar ta Tofa a majalisar wakilai ta Kasa.

I

Leave a Reply

%d bloggers like this: