Jam’iyyar NNPP a Kano ta lashe zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 44 da kansiloli a jihar

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Kano Farfesa Sani Malumfashi ne ya bayyana haka a yau.


Ya ce an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana.
A cewarsa, sun samu haɗin kai daga wurare daban-daban a jihar ciki har da kungiyoyi masu zaman kansu.
Farfesa Malumfashi ya ce zaben da aka yi an irga kuri’a kuma aka tabbatar da jam’iyyar NNPP ce ta lashe dukkanin kujerun.
Idan za a iya tunawa wata babbar kotun jihar Kano ce ta bai wa hukumar zaɓen izinin gudanar da zaɓen, bayan samun umarni daga kotun tarayya da ta hana.
Saidai wata kotun tarayya ta sake bayar da umarnin hana zaɓen wanda aka yi a yau.