Shugaban Rukunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa matatarsa na da karfin samar da man fatur din da ke buƙata a fadin Najeriya.

Dangote ya bayyana hakan ne ga manema labarai jim kadan bayan kammala ganawa da shugaba Tinubu a fadarsa da ke Abuja a yau Talata.

Dangote ya ce ana buƙatar litar man fetur miliyan 30 zuwa 32 a kowace rana a Kasar.

Alhaji Aliko ya ce za su iya samar da duk man da ake buƙata a Kasar, inda ya ce a kiyasi ana shan kusan lita miliyan 32 zuwa 39.

Dangote ya kara da cewa a halin yanzu su na da lita miliyan 500 a ma’ajiyarsu, inda ya ce ko da ba su ci gaba da samar da man ba, ko kuma ba a shigo da fetur ba zai wadatar da ƙasar har zuwa nan da kwanaki 12.

Dangote ya ce sun shirya tsaf, kuma ya gayawa shugaban Tinubu cewa za su iya samar da fetur lita miliyan 30 kowace rana akasuwa a Kasar.

Acewar Dangote za a daina samun dogayen layuka a gidajen mai matukar dillalan mai suka fara sayen mai kai tsaye daga matatarsa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: