Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da naira 71,000 a matsayin sabon mafi karancin ga ma’aikatantan Jihar.

Gwamna Abba ya bayyana hakan a yau Talata a gwamnatinsa da ke Jihar, bayan ganawa da wakilan Kungiyar ƙwadago.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, gwamnan ya ce sabon mafi karancin albarshin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Nuwamba mai kamawa.

